News
Tsadar Rayuwa: Masu Zanga-zanga Sun Datse Hanyar Shiga Abuja Yayin Da Sojoji Sun Kafa Shinge Kan Titin Abuja
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dandazon masu zanga-zanga a safiyar ranar Litinin sun datse babban titin da ya tashi daga Zuba zuwa Kaduna.
Sun datse daidai Kaduna Road, kusa da Zuba a Jihar Neja, lamarin da hakan ke nuni da cewa hasalallu sun kasa haƙura ranar Alhamis 1 ga Agusta ta yi, ranar da aka tsara fara zanga-zangar ta kwanaki 10.
Yawancin masu zanga-zangar dai su na neman gwamnatin tarayya ta sauƙaƙa wa mutane raɗaɗin tsadar rayuwar da ke gallabar su, tun daga ranar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya hau mulki, inda ya cire tallafin man fetur.
Masu zanga-zanga sun riƙe kwalaye daban-daban masu ɗauke da rubutu daban-daban kamar, ‘Mu Fa Ba Bayin Ku Ba Ne’, ‘Tura Fa Ta Kai Bango’, ‘A Cire Duk Wasu Tsare-tsaren da Ba Su Da Alfanu Ga Talaka’, ‘Tilas Sai An Dawo Da Tallafin Fetur.’
Gwamnatin Tinubu dai ta ce tsare-tsaren da ta bijiro da su za su zame wa ‘yan Najeriya alheri nan gaba.
To sai dai kuma talakawa ba su ga alamun haka ba, yayin da a kullum sai kayan abinci ya samu ƙarin tashin farashi, kuma rayuwa sai ƙara tsada take yi.
A gefe ɗaya kuma talakawa na ganin har yanzu gwamnati ba ta rage facaka da kuɗaɗe ba, duk kuwa da matsalar rashin kuɗin da take kuka da shi.
Zanga-zanga: Sojoji Sun Kafa Shinge Kan Titin Abuja Zuwa Keffi:
Da safiyar yau Litinin aka wayi gari Sojojin Najeriya sun kafa shingen binciken motoci masu sammakon shiga Abuja daga kan hanyar Keffi.
Motocin da ke shiga Abuja daga Jos, Keffi, Nasarawa, Maraba, Nyanya da sauran garuruwa sun fuskanci tsaikon dogon lokaci, ta yadda jerin motoci ya kai kusan kilomita 12.
Ma’aikatan gwamnatin tarayya da sauran ma’aikata da dama tilas ta sa sun haƙura sun koma gida, sun fara shiga Abuja, saboda motoci sun yi tsaye cak.
Premium Times
