Connect with us

News

Gargadi Ga Wadanda Ke Karatu A Kwalejojin Kimiyya Da Fasaha (Polytechnic) Daga Hukumar NYSC

Published

on

Yan bautar kasa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) ta yi gargadin cewa wadanda suka kammala karatu a Kwalejojin kimiyya da fasaha ba tare da shaidar kammala horo na shekara daya (IT) ba ba za a tura su aikin yi wa kasa hidima ba.

Advertisement

Yetunde Baderinwa, Ko’odinetan NYSC a Jihar Legas ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Asabar a Legas.

Zanga-Zangar Da Aka Yi A Najeriya DA Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane Tare Da Lalata Biliyoyin Kudi Ba Dimokuradiyya Ba Ce —Dr Abbati Bako

Baderinwa ta ce hukumar NYSC ta fitar da sanarwa a kan hakan.

Advertisement

Baderinwa ta ce: “An lura cewa wasu dalibai da ke karatu a kwalejojin kimiyya da fasaha ba sa kiyaye wajabcin yin aikin horo na IT na shekara daya kafinsu dawo kammala karatun su na HND.

“Dole sai mutum ya yi shekara daya na horo, wato IT shine sharadi na HND.

Advertisement

“Dole ne su yi aikin IT na shekara guda tare da shaidar kammala karatunsu kafin su tafi HND, kuma dole ne hukumomi su tabbatar da hakan kafin a shigar da su HND.

Duk wanda ba shi da wannan shaida ba za a tura shi aikin bautar kasa ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending