News
Gwamna Kano Abba Kabir Ya Janye Dokar Taƙaita Zirga-zirga Baki Ɗaya A Jihar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanar da janye dokar hana zirga-zirga baƙi ɗaya, biyo bayan samun dai-daituwar al’amura a faɗin jihar, domin al’umma su ci gaba da gudanar da zirga-zirgar su ta yau da kullum.
Da yake jawabi yayin ayyana janye dokar gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa biyo bayan ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro da ke faɗin jihar, hakan ne ya tabbatar da cewa al’amura sun dai-daita har ma aka janye dokar.
Da Ɗumi-Ɗumi: WAEC Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar WASSCE Ta Shekarar 2024
“Muna Allah wa-dai ga matasan da suka yi amfani da lokacin zanga-zangar lumana wajen shiga babbar kotun jiha da ke cikin Audu Bako, da suka lalata dukkannin abubuwan da suke ciki da kuma sace kayayyaki da dama, “in gwamna Abba Kabir”.
Rahotanni na nuni da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar musamman ma Matasa, da su dai na biyewa wasu suna sanya su aikata laifuka, kuma gwamnatin sa za ta tabbatar da samar da wasu hanyoyi da zasu dogaro da kan su.
