Connect with us

News

 Jami’an Tsaro Sun Gayyaci Shugaban NLC Kan Zargin Tallafa Wa Ta’addanci

Published

on

Yan sanda sun gayyaci shugaban NLC kan zargin tallafa wa ta’addanci
Shugaban Kungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rundunar ƴan sanda ta gayyaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero kan zarginsa da hannu a cikin ɗaukar nauyin ta’addanci da wasu laifukan da suka shafi sata a Najeriya.

Advertisement

Cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda, IRT ya fitar, rundunar ta umarci Ajaero ya hallara a ofishin IRT a ranar Talata 20 ga watan Agusta.

Kungiyar ASUU Ta Fitar Da Sanarwar Tafiya Yajin Aiki Nan Da Kwanaki 21

Sanarwar ta ce, “wannan ofishin na bincike kan laifukan makircin fashi, ɗaukar nauyin ta’addanci, zamba cikin aminci, maƙarƙashiya da sata ta yanar gizo waɗanda aka ambaci sunanka.”

Advertisement

Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa, za a kama shi matuƙar ya ƙi amsa wa kiran da aka masa.

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending