News
Zargin Ta’addanci: ‘Zamu Tafi Yajin Aiki Idan ‘Yan Sanda Sun Tsare Ajaero’ – Kungiyar NLC
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙungiyar kwadago ta kasa NLC,ta yi barazanar tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar nan idan har rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tsare shugabanta na kasa, Joe Ajaero.
Ƙungiyar tayi barazanar shiga yajin aikin ne a yau Talata a shelkwatar ta bayan taron gaggawa da kwamitin ƙoli na kungiyar na kasa ya gudanar don tattauna gayyatar da ‘yan sanda suka yiwa shugaban NLC kan zargin daukar nauyin ta’adannci.
Ƙungiyar ta ce Ajaero zai amsa gayyatar ‘yan sandan sai dai mai bai wa kungiyar shawara a fannin shari’a zai nemi karin lokaci kafin shugaban na NLC ya bayyana gaban rundunar yan sandan.
Comrade Ado Kabiru Sani, mataimakin shugaban NLC na kasa ya bukaci ma’aikata da su zauna da shirin ko ta kwana idan ‘yan sanda suka tsare Ajaero.
