News
An Tsinci Jaririyar Da Aka Yar A Kan Titi A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An tsinci jaririyar da aka yar a kan titi a unguwar ‘Yar-akwa da ke Na’ibawa a karamar hukumar Tarauni dake Kano.
Wasu mutane dake shagon siyar da shayi ne suka ji kukan jaririyar inda suka gaggauta zuwa wurin.
Jami’an Tsaro Sun Ruga Da Sun Zama Karnukan Farautar Gwamnatin Tarayya _ Kwamared Nasir Kabir
“Da farko, mun zaci mage ce, amma bayan bincike. Mun hangi masu gadi da jaririyar,” inji wani shaidar gani da ido mai suna Shamsudeen Sabiu.
Mai unguwar ‘Yar Akwa, Jamilu Abba Danladi, ya tabbatar da karbar jaririyar inda ya bayyana farin ciki saboda samun jaririyar da rai cikin koshin lafiya.
Mahukunta sun ce suna bincike kan dalilin faruwar lamarin kuma suna aiki don gane mahaifiyar jaririyar.
Sannan sun bukaci, duk wanda ke da bayani game da mahaifiyar jaririyar ya sanarwa da hukumomi
DAILY NIGERIAN
