Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malaman Asibiti Da Marasa Lafiya A Jihar Kaduna

Published

on

DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN TUKUNTAWA

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a wani ƙaramin asibitin gwamnati (PHC) da ke Kuyallo a ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da malaman asibiti biyu da marasa lafiya da ba a tantance adadinsu ba.

Advertisement

A lokacin haɗa rahoton, ba a samu wani jawabi daga rundunar ƴan sandan jihar ko jami’an gwamnati ba duk da ƙoƙarin neman Kakakin ƴan sanda, ASP Mansir Hassan da aka yi da sakonni da aka aika masa.

An Tsinci Jaririyar Da Aka Yar A Kan Titi A Kano

Da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Litinin ne suka kai hari a makarantar sekandire da ke kusa da garin inda suka samu babu kowa, saboda haka sai suka sauya akalarsu zuwa asibitin, kamar yadda shugaban ƴan banga, Musa Alhasan ya shaidawa manema labarai.

Advertisement

Shaidu sun bayyana cewa, ƴan ta’addar sun shigo yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai inda suka yi garkuwa da mutanen.

Kawo yanzu dai, waɗanda suka yi garkuwa da Dakta Ganiyat Popoola wacce likita ce da ke tsare a hannun su tsawon watanni ba su sako ta ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending