Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Madatsan Ruwa Biyar Domin Tare Ruwan Dam Ɗin Lagdo

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

DAGA MUHAMMAD ZAHRADDIN

Gwamnatin Tarayya ta bakin Hukumar Ruwa ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency (NIHSA) ta ce za ta gina wasu madatsun ruwa biyar domin kare ambaliyar da ke faruwa a sanadiyar ruwan da ke mamal daga dam ɗin Lagbo na Kamaru.

Advertisement

Darakta-Janar na NIHSA, Umar Mohammed ne ya bayyana hakan a zantawarsa ta talabijin na Channels a ranar Alhamis.

Mafi Ƙarancin Albashi: Duk Ma’aikatar Da Ta Ke Biyan Ma’aikata Ƙasa Da N70,000 Za Ta Ɗanɗana Kuɗar Ta  —Gwamnatin Tarayya

Hukumar ta gargaɗi ƴan Najeriya da suke zaune a wuraren da ake ambaliya su canja mazauni saboda sako ruwan da aka yi daga Kamaru.

Advertisement

PRNIGERIAN ta ruwaito cewa Jihohin da ake fargabar dam ɗin na Kamaru zai jawo ambaliya sun haɗa da Adamawa da Taraba da Benue da Nasarawa da Kogi da Edo da Delta da Anambra da Bayelsa da Kuros Riba da Rivers.

Mohammed, wanda daraktan aikace-aikace na hukumar Femi Bejide ya wakilta, ya ce hukumar ta miƙa wa Fadar Shugaban Ƙasa rahoto, inda a ciki ta bayyana hanyoyin da za a kiyaye aukuwar ambaliyar, ciki har da sauya wuraren da wasu dam suke.

Advertisement

“Sannan mun miƙa buƙatar gina wasu dam guda biyar domin tare ruwan dam ɗin Lagdo,” in ji shi.

“Amma dole za a canja inda wasu dam suke, sannan a faɗaɗa gaɓar tekunan Neja da Benuwe.”

Advertisement

Sako ruwan dam ɗin Lagdo ya zo ne kwanaki kaɗan bayan dam ɗin Alau a Maiduguri ya yi ambaliya, inda aƙalla mutum 30 suka mutu, sannan ya raba dubbai da muhallansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending