Connect with us

News

Mafi Ƙarancin Albashi: Duk Ma’aikatar Da Ta Ke Biyan Ma’aikata Ƙasa Da N70,000 Za Ta Ɗanɗana Kuɗar Ta  —Gwamnatin Tarayya

Published

on

Mafi Ƙarancin Albashi Duk Ma'aikatar Da Ta Ke Biyan Ma'aikata Ƙasa Da N70,000 Za Ta Ɗanɗana Kuɗar Ta —Gwamnatin Tarayya

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Gwamnatin tarayya ta gargadi ga ma’aikatu masu zaman kansu da su dena biyan ma’aikata albashi ƙasa da sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Advertisement

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Babban sakatare na ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya, Alhaji Ismaila Abubakar, ne ya yi wannan gargadin a jiya Laraba, a jihar Legas, yayin da ya ke jawabi a wajen taron shekara-shekara na kungiyar ma’aikata ta ma’aikatu masu zaman kansu na Najeriya karo na 13.

Mafi Ƙarancin Albashi: Duk Ma’aikatar Da Ta Ke Biyan Ma’aikata Ƙasa Da N70,000 Za Ta Ɗanɗana Kuɗar Ta  —Gwamnatin Tarayya

Abubakar, wanda Darakta mai kula da ayyukan yi da albashi na ma’aikatar ,John Nyamali ya wakilta, ya ce yanzu haka mafi ƙarancin albashi ya zama doka.

Advertisement

Ya ce: “A yanzu mafi karancin albashi ya zama doka, saboda haka, laifi ne kuma hukunci na nan ga duk wata ma’aikata da ta ke biyan ma’aikata kasa da N70,000 na mafi ƙarancin albashi.

“Ma’aikatu masu zaman kansu su wajabta wa kan su a wajen duk wata kwangila da za su karba daga hannun wasu cewa kada ma’aikatansu su rika samun kasa da mafi karancin albashi. Ma’aikaci ya kamata ya rika daukar N70,000 mafi ƙarancin albashi bayan an yi duk wasu cire-cire na haraji,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending