News
Wani Jami’in Gidan Yari Ya Kashe Abokin Aikinsa Bayan Wata ‘Yar Hatsaniya Kan Abinci
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani jami’in gidan gyaran hali da ke aiki a gidan gyaran hali na Burra wato gidan yari, Jihar Bauchi, ya kashe abokin aikinsa bayan wata ‘yar hatsaniya kan abinci.
WikkiTimes ta tattaro cewa lamarin ya faru ne ranar Talata 17 ga Satumba 2024, da misalin karfe 2 na rana a garin Burra, cikin karamar hukumar Ningi.
Gwamnan Kano Abba Kabir ya soke Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, mamacin, Aliyu Abubakar Chiroma, da abokin aikinsa, Kabiru Abubakar, sun kasance abokai makusanta da aka sansu sosai a gidan gidan Yarin.
Ɗaurin Shekaru 14 ne Hukuncin Masu Digirin Bogi Ƴar Kwatano
Sun fara rikici ne lokacin da Aliyu Abubakar Chiroma ya kawo abincinsa na rana, sai abokinsa Kabiru ya dage cewa lallai sai ya ci abincin duk da cewa Chiroma bai yarda ba, lamarin da ya janyo barkewar rikici a tsakanin su.
“Sun fara cacar baki wanda daga bisani ya kai ga fada. Kabiru ya gwari Aliyu Chiroma da kansa, wanda hakan ya sa ya fadi kasa. Hayaniyar ya sa mutane suka taru a wurin,” in ji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa an garzaya da Aliyu zuwa Babban Asibitin Burra, inda aka tabbatar da rasuwarsa duk da kokarin da aka yi na ceto rayuwarsa.
Hukumomi sun tabbatar da faruwar lamarin
Shugaban karamar hukumar Ningi, Hon. Nasiru Zakari, ya tabbatar da faruwar lamarin ga WikkiTimes a wata hira da suka yi ranar Alhamis.
Ya ce, “Na samu rahoton wannan mummunan lamari a gidan gyaran hali na Burra, inda ake zargin wani jami’i da kashe abokin aikinsa saboda wata rashin jituwa a lokacin cin abincin rana.”
An Daure Wani Mutum Da Ya Yi Karyar Hada Auren Sirikarsa Da Buhari
Kakakin hukumar gidan gyaran hali na jihar Bauchi, Ahmad Usman Tata, ya kuma tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce abin ya faru ne a wajen gidan gyaran halin.
Ahmad ya bayyana cewa Chiroma, mamacin, dan asalin karamar hukumar Giade ne, yayin da wanda ake zargi, Kabiru Abubakar, shi kuma daga karamar hukumar Dass yake duk a jiharBauchi, wadan da an tura suke aiki a gidan gyaran hali na Burra.
Ya kara da cewa an mika gawar mamacin ga iyalansa don yin jana’iza, yayin da wanda ake zargi ke hannun ‘yan sanda don gudanar da bincike.
Kokarin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi, Ahmad Wakil, abin yaci tura, domin bai amsa tambayoyin da aka yi masa ba.
