News
Ba Za Mu Bari Shirin DRF Ya Durkushe Ba Saboda Dimbin Alfanun Da Yake Da Shi Ga Al’umma — Dr. Labaran
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An ba wa al’ummar jihar Kano tabbacin cewa shirin (DRF) da ke samar da magunguna masu araha da masu inganci da kuma hanyoyin da za a iya amfani da su a cibiyoyin kula da lafiyar jama’a, ba za mu bari ya durkushe ba saboda dimbin alfanun da yake da shi ga al’umma.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya tabbatar da hakan a jawabinsa na bude taron kwana 3 na Shirin DRF ga masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jihar Kaduna.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar INDA RANKA
Sanarwar ta kara da cewa taron yana da manufofin bayar da ra’ayi ga manyan masu ruwa da tsaki game da yadda ayyukan Shirin DRF da ke gudanarwa a Hukumar Kula da Asibitoci, Hukumar Kula da Lafiya A Matakin Farko, da Hukumar Kula da Magunguna .
Dakta Labaran ya ce taron ya zo a daidai lokacin da ya dace domin a shekara mai zuwa shirin DRF za ta yi bikin cika shekaru 20 da fara aiki a Kano ya kara da cewa duk da dimbin kalubalen da shirin ke fuskanta tsawon shekaru, amma duk da haka yana ci gaba da yin karfi a kowace rana.
Ya ce zuwa yau sama da jihohi 21 ne ke gudanar da aikin DRF a Najeriya saboda nasarorin da Kano ta samu kawo yanzu. Kuma da yawa daga cikin samfuran DRF da ake amfani da su a matakin kasa daga Kano ake kwafi, kuma muna samun yabo a duniya.
Daga nan sai ya bukaci kwamitin na SHCSS da ya gaggauta samar da hanyoyin da za a bi wajen kara sanya ido da kuma kula da cibiyoyin kiwon lafiya da ke aiki da DRF.
Kwamishinan ya tabbatar wa da kwamitin kudirin siyasa da goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci gwamnati kan duk wani shiri, wanda a karshe ya kai ga inganta kulawar al’ummar jihar Kano.
Dr. Labaran ya yabawa kungiyar Global Affairs Canada Nutrition International Ingancin Sakamakon saboda tallafin da suke bayarwa na tsarin samar da abinci na jihar, yana mai ba su tabbacin ci gaba da aiki mai jituwa saboda sha’awar su na ganin tsarin kiwon lafiyar jihar ya kasance daidai.
