News
Kotu Ta Yanke Wa Dan Shekara 80 Hukuncin Daurin Shekaru Bakwai A Gidan Yari A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata babbar kotu da ke zamanta a Kano ta yanke wa Ya’u Abdullahi dan shekara 80 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari sakamakon samunsa da laifin lalata da wata yarinya mai shekaru 8.
Kamfanin Dallancin Labarai Na Kasa NAN ta ruwaito cewa Hukumar hana fataucin mutane ta kasa reshen jihar Kano,(NAPTIP) ce ta gurfanar da Abdullahi a gaban kotu.
KANO: Shiga Zanga Zanga Ba Zai Kawo Karshen Tsadar Rayuwar Da Ake Cike Ba —Kwamitin Zaman Lafiya
Mai shari’a S M Shu’aibu, ya ce lauyan masu shigar da kara ya tabbatar da lamarin ba tare da ja In Ja ba.
“Kotu ta yankewa Ya’u Abdullahi hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan kaso babu neman tara”
Tun da farko, lauyan masu gabatar da kara kuma kwamandan shiyyar Kano NAPTIP, Mista Abdullahi Babale, ya shaida wa kotun cewa kungiyar ‘yan banga reshen Kano Metropolitan ita ce ta kai rahoton faruwar lamarin a ranar 27 ga watan Agusta.
Haka zalika WIKKI TIMES ta ruwaito cewa wanda ake kara tabbas ya aikata laifin tun a ranar 26 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 8:00 na dare a kasuwar Murtala da ke karamar hukumar Nassarawa a Kano.
Haka kuma wanda ake tuhumar ya yi nasarar aikata aika-aikan ne ta hanyar yaudarar yarinyar inda ya ja ta zuwa wani kebantaccen wuri.
Lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da bayanan wanda ake kara da kuma na wadanda suke karar cikin harshen Hausa da turanci.
Haka kuma Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake karar sa akai.
Lauya Mai gabatar da kara ya bayyana cewa laifin ya ci karo da tanadin sashe na 16(1) na dokar hana fataucin mutane na shekararar 2015 da kuma hukunci a karkashin sashe na 26(1) na TIP ACT 2015.
Sai Dai Lauyan Wanda ake kara Hajiya Fatima Chabir, ta roki kotu da ta yi wa Abdullahi sassauci
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
