News
Makaman Da Ke Hannun Ƴan Ta’adda da ƴan bindiga A Najeriya Mallakin Gwamnatin Tarayya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Akasarin haramtattun makaman da ke hannun ƴan ta’adda da ƴan bindiga a Najeriya, mallakin gwamnatin ƙasar ne kamar yadda Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Lamurran Tsaro, Mallam Nuhu Ribaɗu ya bayyana.
Ribaɗu na magane a birnin Abuja a wurin taron lalata makamai da Cibiyar Daƙile Yaɗuwar Ƙananan Makamai ta Ƙasa ta shirya.
Arzikin Aliko Dangote ya ninka zuwa dala biliyan 28 bayan matatar mansa ta fara aiki
A cewar Ribaɗu, waɗannan makaman sun faɗa hannun ɓata-gari ne saboda wasu gurɓatattun jami’an tsaron Najeriya.
Kodayake ya ce, ƙasar na da ikon tunkarar lamurran tsaronta.
Za mu lalubo hanyar kawo ƙarshen wannan lamari. Dole ne mu farfaɗo da ƙasarmu domin rayuwa cikin zaman lafiya
Ribaɗu ya bayyana cewa, mafi munin ɓata-garin shi ne jami’in ƴan sanda ko soja da ke ɗaukar makamai yana sayar da su ko ɓoye su ga miyagun da ke kashe masa abokan aiki.
Dole ne mu yaƙi waɗannan mutanen, kodayake akwai wasu ɓata-garin daga wasu wuraren. Yaɗuwar haramtattun ƙananan makamai na ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron ƙasarmu, lamarin da ke tsananta ta’addanci da ayyukan ƴan bindiga da sauran miyagun laifuka. Inji Ribaɗu.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
