Connect with us

News

Aƙalla Mutum Bakwai Ne Suka Rasu Sakamakon Ruhsewar Gini A Abuja

Published

on

1000192925

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu sakamakon ruhsewar wani gini a babban birnin tarayya Abuja.

Advertisement

Muƙaddashin daraktan  hukumar bada agajin gaggawa ta Abuja FEMA, Abdulrahman Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara wajen ginin da ya rushe a kan titin hanyar tafiya filin jirgin sama.

Amarya Ta Fasa Auren Saurayin Ta Ranar Aure Kan Ƙin Saya Mata Wayar ₦150,000 

Channels ta ruwaito cewa ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar a sanadiyar wasu da suka shiga ginin, wanda hukumar kula da ingancin gine-gine ta Abuja take rusawa domin cire ƙarafa.

Advertisement

Ya ce bayan waɗanda suka rasu, akwai wasu mutum da suke jinya a asibiti, sannan ya gargaɗi mutane su guji jefa rayukansu cikin hatsari ta hanyar shiga cikin gine-ginen da aka rusa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending