News
Nan Da Kwanaki Biyar Wutar Lantarki Zata Dawo A Arewacin Najeriya – Kamfanin TCN
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Bayan katsewar wutar lantarki sama da mako guda , Kamfanin dake rarraba wutar lantarki a Najeriya TCN yayi alkawarin cewar nan da kwanaki biyar za’a gama gyaran matsalar rashin wuta a Arewacin Najeriya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya sanar da cewa, za a kammala gyaran layukan da suka lalace a arewacin Najeriya nan da ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba, 2024.
Manajan Daraktan TCN Alhaji Sule Abdulaziz shine ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau Talata a Abuja, inda ya bayyanawa ‘yan Najeriya kokarin da sukeyi dan dawo da wutar lantarki a yankin Arewa.
A ranar 22 ga watan Oktoba, TCN ya bada rahoton katsewar wutar lantarki a arewa maso gabas arewa maso yamma, da kuma wasu sassan arewa ta tsakiyar. Najeriya bayan da layin wutar lantarki mai tsawon kilo 330 na Ugwuaji ya sami matsala.
Bugu da kari, TCN ya ruwaito cewa an lalata layin Shiroro zuwa Kaduna, wanda hakan ya sa aka rage yawan wutar lantarki a Kaduna, Kano, da sauran manyan birane a Arewa.
Bayan kwanaki biyu, kamfanin TCN ya bayyana cewar layin mai karfin 330kv daya Sani matsala a cikin dajin Igumale na jihar Benue, ya kara taimakawa wajen katsewar wutar lantarkin.
A ranar Litinin, TCN ta bayyana cewa rashin tsaro ya kawo masa cikas wajen jinkirin gyarawa amma kuma ya bada tabbacin cewa yana aiki tukuru don gyaran matsalar gaba daya.
Shugaba Bola Tinubu ya kuma umurci TCN da ta gaggauta gyara sannan ya Kuma umarci mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da ya samar da tsaro ga ma’aikatan da zasuyi aikin.
Da yake bayar da karin haske, Shugaban TCN ya ce kamfanin ya tura injiniyoyinsa don kammala aikin gyaran kuma an shirya raba kusan megawatt 500 zuwa 600 ga yankin arewa nan da ranar Lahadi.
