Connect with us

News

Gwamnatin Kano Tana Sake Gina  Shataletalen Gaban Gidan Gwamnatin Data Rushe A Baya.

Published

on

Gwamnatin Kano tana sake gina hasumayar shataletalen gaban gidan gwamnatin data rushe a baya.

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Kano tana sake gina hasumayar shataletalen gaban gidan gwamnatin data rushe a baya.

Advertisement

A watannin baya ne Gwamnatin jihar Kano, karkashin Engr Abba Kabir Yusuf, ta rushe babbar hasumayar shataletalen gaban gidan jihar, wanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta samar bayan kashe mata makudan kudade wajen gina ta.

Tsangayar Nazari A Fannin Tsaro Ta Akarrama Amb. Ibrahim Waiya Da Lambar Yabo 

A yayin rushewar gwamnatin Kano ta kafa hujja da cewa hasumayar dana dauke da alamar Cross a Samanta, tare da cewa zata iya kawowa gidan gwamnatin barazanar tsaro.

Advertisement

Sai dai a yanzu haka Mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin sake gina hasumayar a dandalin Shari’a dake Kofar Nassarawa da za’a kashe naira miliyan 164.9, wajen sake ginin.

Bayan haka itama Hasumiyar Dandalin Shari’ar za’a matsar da ita gefe kadan kusa da katangar jami’ar Northwest Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending