Connect with us

News

DA DUMI-DUMI: Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Litar Man fetur

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kamfanin matatar Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N899.50 a kowace lita.

Advertisement

Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata takarda da aka fitar da safiyar Alhamis.

Jami’an Hukumar NAFDAC Sun Ankarar Da Jama’a A Kan Wani Jabun Maganin Zazzabin Cizon Sauro

Kamfanin ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin “bada sauki ga ‘yan Najeriya kafin lokacin bukukuwan karshen shekara.”

Advertisement

Matatar mai ta farko mai zaman kanta a nahiyar Afrika, wadda a baya ta rage farashin zuwa N970 a kowace lita a ranar 24 ga watan Nuwamba, yanzu ta sanar da sabon farashi na N899.50k a kowace lita.

Wannan ragin farashin man Fetur na da nufin rage kudin sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara,” in ji sanarwar da Babban Jami’in Yada Labarai na Kamfanin, Anthony Chiejina, ya sa hannu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending