Connect with us

News

Jami’an Hukumar NAFDAC Sun Ankarar Da Jama’a A Kan Wani Jabun Maganin Zazzabin Cizon Sauro

Published

on

NAFDAC Ta Ankarar Da Jama’a A Kan Wani Jabun Maganin Zazzabi A Shaguna

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar kula da sahihanci da ingancin magunguna da abinci a kasa (NAFDAC) ta ankarar da jama’a a kan wani jabun maganin zazzabin cizon sauro mai suna ”Paludex” wanda ake siyar da kwayoyin sa da na ruwa a shagunan magani a fadin Naeriya

Advertisement

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa a wani jawabi da ta fitar a shafin ta na dandalin zumunta ‘X’, NAFDAC ta bayyana cewa maganin, ‘Paludex’, wanda aka nuna ya kunshi sinadaran ‘Artemether/Lumefantrine, wani kamfani ne mai suna ‘Impact Pharmaceutical Ltd, wanda ya ke fili mai lamba 33A/33AB a rukunin masana’antu na Emene a jihar Enugu, ya ke samar da shi.

Gwamnan Kano Ya Zargi Jam’iyyun Adawa Da Rura Wutar Rikicin Siyasa A Kano

Kazalika, jawabin ya bayyana sunan MD Life Sciences Ltd da ke rukunin masana’antu na Emene a jihar Enugu, a matsayin kamfanin da ke kasuwancin maganin.

Advertisement

NAFDAC ta bayyana cewa bayan samfurin maganin na kwaya, akwai wani samfurin Paludex (180mg/1080mg) na ruwa domin amfanin kananan yara.

Hukumar NAFDAC ta ce sakamakon binciken inganci da aka gudanar a dakin gwaje-gwaje na hukumar lafiya ta duniya (WHO) da ke kasar Germany ya nuna cewa babu sinadaran (API) da za su yaki kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro a cikin magungunan.

Advertisement

A cewar jawabin, dukkan magungunan babu su a cikin jerin kayan da hukumar NAFDAC ta taba yi wa rijista tare da bayyana cewa hatta lambar NAFDAC da aka rubuta a magungunan ta karya ce.

NAFDAC ta ce ta sanar da dukkan shugabannin ofisohin ta da ke fadin Nigeria a kan su gudanar da bincike a jihohin su tare da kwacewa da kuma dakile yada maganin duk inda aka gano shi.

Advertisement

Har ila yau, NAFDAC ta yi kira ga manyan ‘yan kasuwar magunguna, ma su aiki a cibiyoyin lafiya, da ma marasa lafiya a kan su lura sosai domin tabbatar da cewa ba a cigaba da amfani da maganin ba.

NAFDAC ta yi kira ga jama’a a kan su guji siyan magunguna a wurare ko shagunan da basu da sahalewa ko lasisi daga hukuma.

Advertisement

A karshe, NAFDAC ta bukaci jama’a su sanar da ita duk wani magani da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin hukumar mafi kusa ko kuma ta hanyar kiran lambar su a kan 0800-162-3322 ko kuma ta hanyar sako a adireshin su na email: sf.alert@nafdac.gov.ng.

 

Advertisement

 

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending