Connect with us

News

Hukumar  KAROTA, Ta Gurfanar Da Mutum 3 Da Ake Zargin Da Cin Zarafin Jami,anta A Kotu 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kula da zirga zirgar Ababen hawa ta jahar Kano KAROTA, ta gurfanar da wasu mutane 3, da ake zarginsu da cin zarafin Jami,anta yayin da suke tsaka da gudanar da aikinsu.

Advertisement

Hukumar ta KAROTA ta shigar da karar Mutanen da suka hadar da Abubakar Mustapha, Najib Idris, da kuma Faruq Dan Alhaji a gaban kotun Noman Islands mai lamba 47, dake Sabon Gari .

Da Yiwuwar Kamfanonin Sadarwa Su Kara Kudin Kiran Waya Da Na ‘Data’ A Farkon Shekarar 2025

Bayan gurfanar da mutanen da ake zargin a gaban kotun Alkalin kotun ya karanto musu tuhumar da akeyi musu na hana Jami,an hukumar gudanar da aikinsu Wanda ya saba da sashi na 79, da kuma sashi na 171 da 242 hadi da sashi na 327 na kundin penal code.

Advertisement

Alkalin Kotun mai zaman nata a Noman slands ya aike da mutane biyun da Sukazo hannu wato Abubakar Mustapha da Najib Idris, tareda bayar da umarnin kamo Faruok Dan Alhaji, Wanda kotun ke nema Ruwa a jallo.

Alkalin kotun yaja kunnen jama,a dasu guji aikata irin wannan abu ga Jami,an tsaro, tareda Jan kunnen Jami,an hukumar KAROTA dasu ringa nuna kwarewa yayin da suke gudanar da aikinsu, kamar yanda kundin dokar hukumar ta tanada.

Advertisement

A karshe shugaban hukumar ta KAROTA Hon, Faisal Mahmud Kabir ya nuna gamsuwarsa da yanda Shari,ar ta gudana, tare da yin kira ga Jama’a dasu kaucewa daukar doka a hannunsu, idan wani sabani ya faru tsakaninsu da Jami,an Hukumar ta KAROT.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending