Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa ‘Yan Najeriya Su Shirya Karin Kudin Wutar Lantarki 

Published

on

TCN Ya samar da sabbin taransfoma a Legas don ƙara inganta hasken wutar lantarki a jihar

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ‘yan Najeriya su shirya karin kudin wutar lantarki a watanni masu zuwa.

Advertisement

Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Dar es Salaam, Tanzaniya, kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

Waiya Ya Kaddamar Da Kungiyar Masu Tallata Aiyukan Gwamnan Kano A Facebook

Verheijen yana halartar taron da Bankin Duniya ya dauki nauyi, inda Najeriya ta gabatar da shirin kashe dala biliyan 32 don inganta hadakar wutar lantarki zuwa shekarar 2030. Ana sa ran masu zuba jari na kashin kansu za su bayar da dala biliyan 15.5, yayin da ragowar kudin zai fito daga gwamnati, Bankin Duniya, da Bankin Raya Afirka.

Advertisement

Verheijen ya ce dole ne a kara farashin wutar lantarki da kusan kaso biyu cikin uku don yawancin kwastomomi domin ya dace da kudin samar da wuta mai inganci a Najeriya.

Ya kara da cewa karin kudin wuta yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da an samu kudin da ake bukata don kula da ingancin wuta da kuma jawo hankalin masu zuba jari a bangaren samarwa da rarraba wuta. Sai dai ya ce dole ne a yi la’akari da tallafin da za a ba marasa karfi domin kada su sha wahala.

Advertisement

“Daya daga cikin manyan kalubalen da muke kokarin warwarewa a watanni masu zuwa shi ne tsallakawa zuwa tsarin farashin wuta da zai dace da tsadar samar da ita,” in ji shi.

Ya ce hakan yana da matukar muhimmanci don tabbatar da cewa bangaren samar da wutar lantarki yana samun kudin shiga da zai jawo hankalin masu zuba jari.

Advertisement

A halin yanzu, ana fuskantar matsin lamba daga kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke fama da bashin da suka tara, suna bukatar a kara farashin wuta domin su farfado da kasuwancinsu.

Tun bayan da aka sayar da kamfanonin samar da wutar lantarki da rarraba ta a shekarar 2013, farashin wutar lantarki da hukumar NERC ke kayyade wa bai dace da tsarin samar da ita ba. Gwamnati tana bayar da tallafi don rufe wani kaso na gibin kudin, amma hakan bai sa kamfanonin sun samu riba ba.

Advertisement

Verheijen ya ce Najeriya tana bukatar manyan jari a bangaren wutar lantarki don cimma burinta na ci gaba. Daga cikin megawatt 14 na wutar lantarki da ake da ita, megawatt 8 ne kadai ake iya rarrabawa a fadin kasar, yayin da megawatt 4 zuwa 5 ne kawai ke isa kai tsaye zuwa gidaje da wuraren kasuwanci.

Kamfanin Siemens AG yana aiki tare da gwamnati kan wani aikin dala biliyan 2.3 domin inganta tsarin watsa da rarraba wutar lantarki. Har ila yau, sama da ‘yan Najeriya miliyan 7 a yankunan karkara sun samu wutar lantarki ta hanyar ayyukan makamashi mai sabuntawa.

Advertisement

“Dole ne manufofin makamashin kasarka su yi daidai da burin da kake da shi,” in ji Verheijen. “Burina shi ne mu zama kasa da tattalin arzikin da ya kai dala tiriliyan 1 a cikin shekaru biyar, sannan mu zama kasa mai matsakaicin kudin shiga a cikin shekaru 25 masu zuwa.”

A halin yanzu, babban jimillar arzikin Najeriya (GDP) yana kasa da dala biliyan 200, a cewar Hukumar Kudi ta Duniya (IMF).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending