Connect with us

News

Jamhuriyar Nijiar Za Ta  kafa kamfanonin jiragen Sama Mallakinta Da Na Kasashen AES  Domin Tallafawa Fannin Noma Da Kiwo 

Published

on

Mali, Burkina Faso Da Nijar Za Su Ƙaddamar Da Fasfo Ƙarkashin Sabuwar Ƙungiyar Ƙawancensu

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Ministan Sufuri da Kayayyakin Aiki na Nijar Kanal-Manjo Salissou Mahaman Salissou, ya ce nan ba da jimawa Jamhuriyar za ta  kafa kamfanonin jiragen sama da kuma na ƙasashen AES.

 

Advertisement

Kamfanin dillancin labarai na Nijar, ANP, ya ce ministan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ba da bayanai game da ma’aikatarsa a birnin Yamai.

 

Advertisement

“Ƙasarmu na da faɗi sosai, kuma mun bai wa hukumar sufurin jiragen sama (ANAC) umarnin saussauta wasu dokoki domin taimakawa wajen samar da waɗannan kamfanonin. Saboda haka, ANAC ta fitar da sharuɗɗan samun damar wucewa ta sararin samaniya da sauri da kuma damar sauka a ƙasar,” in ji ministan.

 

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa an sauƙaƙa hanyoyin samun takardun shaidar ayyukan jiragen sama a ƙasar.

 

Advertisement

Kazalika kamfanin dillancin labaran Nijar ya ambato ministan yana cewa an riga an kafa kwamiti domin gaggauta bayar da takardun da ake buƙata wajen samar da waɗannan kamfanonin.

 

Advertisement

Ministan ya ce wannan aikin , “wani ɓangare ne daga cikin dabarun duniya na buɗe (ƙasar) domin ƙarfafa hanyoyin da suka haɗa Nijar da makwabtanta da kuma sauƙaƙa sufuri a cikin ƙasar.”

 

Advertisement

“Maƙasudin wannan shi ne tallafa wa fannin noma da kiwo domin bai wa manoma damar sayar da kayayyakinsu cikin aminci,” a cewar ministan.

 

Advertisement

Ministan sufurin ya ce, “yana da muhimmanci a samu ƙwararrun ma’aikata da kuma kayayyakin aiki wajen aiwatar da wannan aiki kuma mun yi sa’a saboda muna da wannan ƙarewar.”

 

Advertisement

“Kafa kamfanin jiragen saman tarayyar AES na cikin abubuwan da muka saka a gaba,” in ji ministan yana mai ƙarawa da cewa “wannan aikin na ci gaba cikin sauri kuma insha Allahu na ba da jimawa ba za mu samu wani kamfani mai kalan AES wanda zai haɗa manyan biranenmu tare da wasu wurare “.

 

Advertisement

Kamfanin ANP ya kuma ambato ministan yana cewa ƙasarsa za ta kafa wata tashar jiragen ruwa ta kan tudu da kuma layin dogo a Maradi da Agadez.

 

Advertisement

Ministan ya ce samar da waɗannan ababen more rayuwar dama ce ga ƙasar Nijar a fagen haɗin kai a yankin da kuma cin gashin kai.

 

Advertisement

Ya ce tattaunawa game da tashar jirgin ruwa ta kan tudu ta Dosso ta sa an rattaɓa hannu kan yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki ciki har da Nijar da Benin domin ayyana makomar tashar.

 

Advertisement

Ya kuma ce kafa wannan tashar jirgin ruwa ta tudun zai sa a fara wani ɓangare na babban layin dogo.

 

Advertisement

Bugu da ƙari, ya ce a wani ɓangare na gina layin dogon, aiki na tafiya kan wani layin dogo daga Nijeriya zuwa Maradi bisa sharruɗan da shugaban ƙasa ya bayar kuma an fara tattaunawa da ‘yan kasuwa domin su taka muhimmiyar rawa wajen kafa wannan tashar jiragen ruwa ta kan tudun

 

Advertisement

Ya ƙara da cewa gina tashar jiragen ruwa na tudu a Agadez yana da alaƙa da ƙarasa gina layin dogo daga Ingazam zuwa Agadez, lamarin da zai ƙarfafa kayayyakin sufuri a yankin.

 

Advertisement

TRT AFRICA HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending