News
Yadda Obasanjo Ya Kori ’Yarsa Daga Gonarsa Saboda Ta Makara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda ya kori ’yarsa daga gonarsa saboda ta makara wajen zuwa aiki, lamarin da ya girgiza ma’aikatan gonar.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da sabon Shugaban Hukumar Kula da Asibitin Tarayya (FMC) na Idi-Aba, Abeokuta, Dr. Dayo Israel, ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke Olusegun Obasanjo Presidential Library, Abeokuta.
Falana Ya Kai Karar Mark Zuckerberg, Yana Neman Dala Miliyan 5 Kan Take Hakkin Sirrinsa
A cewarsa, dole ne shugaba ya kasance mai jajircewa wajen aiwatar da doka ba tare da nuna bambanci ba. Ya ba da misali da yadda ya dauki ’yarsa aiki a gonarsa domin ta samu kwarewar aiki yayin hutu, amma ya kore ta bayan ta makara a rana ta biyu.
“A rana ta farko, ta zo da karfe 7:15 maimakon 7:00. Na gargade ta cewa dole ne ta zama abin koyi ga sauran ma’aikata. Amma a washegari ta sake makara, nan take na dakatar da ita daga bakin kofa,” inji Obasanjo.
Ya ce wannan mataki ya bai wa sauran ma’aikata mamaki, inda suka fahimci cewa yana da tsauri kan ka’idojin aiki.
A nasa jawabin, Dr. Dayo Israel ya jinjinawa Obasanjo, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai basira da hikima.
