News
Falana Ya Kai Karar Mark Zuckerberg, Yana Neman Dala Miliyan 5 Kan Take Hakkin Sirrinsa
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Babban lauya mai kare hakkin bil’adama kuma Babban Lauyan Najeriya (SAN), Mista Femi Falana, ya shigar da kara a babbar kotun Legas kan Meta Platforms Inc., kamfanin fasaha na Amurka mallakar Mark Zuckerberg, bisa zargin take masa haƙƙoƙin sirrinsa.
A cikin karar da aka shigar bisa tanadin Sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), da Sashe na 24(1)(A) da (E) da Sashe na 34(1)(D) na Dokar Kare Bayanai ta Najeriya ta 2023, tare da dokokin gabatar da bukatun kare hakkin dan Adam na 2009, Falana, ta hannun lauyansa Olumide Babalola, ya zargi Meta da wallafa wani bidiyo da sauti mai taken “AfriCare Health Center” a shafinsu, yana nuna cewa yana fama da cutar prostatitis.
An Kama Fasto Da Laifin Safarar Bindigu Zuwa Hannun Ƴan Ta’adda A Filato Da Kaduna
Falana ya bayyana cewa wannan wallafa ta ci zarafinsa, kuma ta take masa hakkin sirri da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada. Ya ce bidiyon da aka wallafa a shafin www.facebook.com ba gaskiya ba ne, kuma yana cike da bayanan karya da suka bata masa suna.
Abubuwan da Falana ke Nema daga Kotu
1. Bayyana cewa wallafa sunansa, hotunansa da sautin da ke cikin bidiyon “AfriCare Health Centre” take masa hakkin sirri, wanda Sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
2. Umartar Meta da ta gaggauta cire bidiyon daga dandalinsu.
3. Biya shi diyya ta dala miliyan biyar ($5,000,000) saboda illar da wallafar ta yi masa.
Zargin Falana Kan Illar Wallafar
Falana ya bayyana cewa wannan wallafa ta bata masa suna, ta rage masa mutunci, kuma ta haddasa masa damuwa da kunci. Ya ce yana da hakkin zaman lafiya da kare sirrinsa, amma Meta ta take wannan hakki ta hanyar wallafa bayanai marasa tushe game da lafiyarsa.
A cikin shaidarsa, ya ce ya gano bidiyon a ranar 16 ga Janairu, 2025, kuma yana dauke da hotonsa da sautin da ke cewa:
> “Suna na Femi Falana, kuma na shafe shekaru 16 ina fama da cutar prostatitis. Tun ina da shekara 50 aka gano ina da wannan cuta. Kowace rana ina fama da zafi, rashin jin dadi da gajiya. Ina da matsalar fitsari, ciwon baya da wasu alamomi da suka hana ni rayuwa mai kyau. Duk da ganin likitoci mafi kyau a kasar nan, ba wanda ya iya warkar da ni.”
Falana ya musanta wannan batu gaba daya, yana mai cewa bai taba fama da wannan cuta ba, kuma bai taba hulɗa da Meta a kan batun lafiyarsa ba. Ya ce wallafar karya ce, kuma ta jawo masa damuwa, bakin ciki, da kuma tozartarwa.
A karshe, Falana ya bukaci kotu ta dauki mataki domin kare sunansa da mutuncinsa daga illar wannan wallafa.
