Connect with us

News

An Kama Fasto Da Laifin Safarar Bindigu Zuwa Hannun Ƴan Ta’adda A Filato Da Kaduna

Published

on

An kama fasto yana kai wa ƴan ta’adda bindiga a Filato da Kaduna

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rundunar ƴan sanda ta samu nasarar cafke wani fasto tare da wasu da ake zarginsu da hannu a safarar bindigu zuwa ga ƴan ta’adda a jihohin Kaduna, Filato, da wasu yankunan Jihar Nasarawa.

Advertisement

Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a lokacin da aka gurfanar da waɗanda ake zargi a makon da ya gabata a Abuja. Ya ce jami’an sashin binciken sirri na IRT a Filato sun kama mutanen a wurare daban-daban, inda aka tabbatar da cewa mambobi ne na wata tawagar safarar muggan makamai.

Yadda Mata Ke Saɓa Wa Al’ada Domin Rufa Wa Kansu Asiri Duk Da Ƙalubalen Da Suke Fuskanta

A yayin wannan aiki na musamman, jami’an IRT sun gano wani rumbun ajiyar makamai tare da ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su.

Advertisement

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Joseph Tata mai shekaru 33, wanda ake wa lakabi da Alias Muazu daga ƙauyen Zumu a ƙaramar hukumar Mikang ta Jihar Filato. Bayanan da aka samu daga gare shi ne suka taimaka wajen cafke Victor Ali-Pam mai shekaru 33, Abua Yusuf, Bako Isa, da Salamatu Ilya ƴar shekara 34, wadda ke zaune a Jos.

Haka kuma, a ranar 28 ga Janairu, jami’an tsaro sun cafke Musa Ari daga Tambegua a Jihar Kaduna da Britus Tom daga Vom a Filato.

Advertisement

Kazalika, an ƙwato bindigu guda takwas ƙirar AK-47, ƙananan bindigu ƙirar pistol, mazubin harsasai, da wasu kayayyakin makamai.

Adejobi ya ƙara da cewa an kama mutanen ne a hanyarsu ta kai makaman ga ƴan ta’adda da ke aikata ta’addanci a yankunan Filato, Kaduna, da kewaye.

Advertisement

 

 

Advertisement

BLUEPRINT

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending