Connect with us

News

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Duba Zargin da Dan Majalisar Amurka Ya Yi — Ndume

Published

on

DAGA MAIMUNA RABIU UMAR 

Tsohon Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Soji, Sanata Ali Ndume, ya bukaci Gwamnatin Najeriya da Majalisar Dokoki da su dauki mataki kan zargin da wani dan majalisar wakilai na Amurka, Scott Perry, ya yi cewa wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa na taimakawa ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.

Advertisement

Ndume, wanda ke wakiltar Jihar Borno, ya bayyana cewa wannan batu ba zargi ne kawai ba, illa kuwa babban abu ne da ke bukatar bincike na gaggawa.

An Kashe Wani Jami’in Hukumar NDLEA Ta Hanyar Kona Shi Kurmus A Kaduna

> “Dole ne gwamnati da Majalisar Dokoki su dauki wannan batu da muhimmanci, su bincika domin tabbatar da ingancinsa.”

Advertisement

Ya tunatar da irin ta’asar da BH suka aikata a Najeriya, ciki har da kai hare-hare kan hedikwatar ‘yan sanda da ofishin Majalisar Dinkin Duniya (UN) a Abuja, wanda ya haddasa asarar rayuka da dama.

A cewarsa, tun a zamanin Laftanar Janar Tukur Buratai, hukumomin tsaro sun taba samun rahotanni kan zargin da ake yi wa wasu kungiyoyin agaji, har ma aka kai farmaki a ofishin USAID ko na UN a Maiduguri.

Advertisement

> “Har gwamnatin jihar Borno ta taba nuna shakku kan ayyukan wasu kungiyoyin agaji. Mun dade muna mamakin daga ina wadannan mutane ke samun kudaden shiga?”

Sanatan ya bayyana cewa sama da mutane 50,000 sun mutu tun daga lokacin da yaki da ta’addanci ya fara kusan shekaru 20 da suka gabata a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga Najeriya da ta daina dogaro da taimakon kasashen waje, yana mai cewa lokaci ya yi da ita ma za ta fara bayar da agaji ga wasu kasashe.

“Muna da komai; matsalarmu kawai ita ce shugabanci. Dole ne mu gyara hakan domin mu kare mutuncinmu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending