Connect with us

News

Al’ummar Rangaza zuwa Bela Sun Bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Cika Alkawarin Gyaran Hanya

Published

on

FB IMG 1739748388380

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Al’ummar garuruwan Rangaza zuwa Bela a Karamar Hukumar Ungoggo sun bukaci Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya cika alkawarin da ya dauka na kammala titin da ya taso daga Dakata, wanda aikin ya tsaya a Rangaza Chalawa zuwa Bela.

Advertisement

A wani gangami da suka gudanar a safiyar yau, al’ummar Rangaza, Inusawa, Adaraye, Zaura Babba, Zaura Danbaba, Yadakunya, da Bela sun bayyana cewa gabatowar damuna ce ta sa su yin wannan gangami domin tunatar da Gwamna matsalar da suke fuskanta a lokacin ruwan sama, kasancewar hanyar bata biyuwa, lamarin da ke jefa su cikin barazana.

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Duba Zargin da Dan Majalisar Amurka Ya Yi — Ndume

Da yake jawabi a madadin al’ummar garuruwan, Shugaban Kungiyar Cigaban Garuruwan, Mujaheed A.D. Mukhtar, ya tunatar da cewa tun lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara Asibitin Bela ya ga halin da suke ciki, ya yi alkawarin kammala titin, amma kawo yanzu babu ci gaba. Ya ce hakan ne ya sa suka shirya wannan gangami domin sake rokon Gwamna ya cika alkawarin da ya dauka, kasancewar rashin titin ya jefa al’ummar yankin cikin matsaloli na tsawon shekaru.

Advertisement

Tattakin, wanda ya faro daga Rangaza Chalawa, ya dangana har zuwa Asibitin Bela, inda mahalarta suka bukaci gwamnatin Kano da ta dauki matakin gaggawa kafin zuwandamuna.

 

Advertisement

 

AREWA RADIO

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending