News
Gwamnatin Kebbi Ta Musanta Rufe Jami’ar Aliero Saboda Cutar Sankarau
Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa ta rufe Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliero sakamakon bullar cutar sankarau, wacce ta yi sanadin mutuwar akalla dalibai 11.
Sai dai gwamnatin ta tabbatar da ɓullar cutar a jami’ar, amma ta ce tuni ta ɗauki matakan dakile yaduwarta.
Mata Da Ke Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga Ta Shiga Komar ‘Yan Sanda
Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Kebbi, Alhaji Isa Abubakar Tugga, ya tabbatar da hakan, yana mai jaddada cewa babu wata umarni daga gwamnati na rufe jami’ar.
Tun jiya Laraba ne dai rahotanni suka cika shafukan sada zumunta da ke cewa an rufe jami’ar saboda cutar sankarau, lamarin da gwamnatin ta ce ba shi da tushe.
Advertisements
