News
Maniyyata 3,155 Sun Yi Rijistar Hajjin Bana Daga Jihar Kano
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da kammala rijistar maniyyata 3,155 da za su gudanar da aikin Hajjin 2025. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin tawagar hukumar shige da fice a ofishinsa.
Ya ce hukumar ta kammala shirye-shiryen da suka shafi takardu da jakunkunan hannu na maniyyatan, sannan a halin yanzu ana kokarin kammala hada bizar su. Haka nan, ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayan da take bai wa hukumar don tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin sauki.
Hukumar Kula da Lafiya A Matakin Farko Ta Sabunta Asibitoci 58 A Jihar Nasarawa
A nata bangaren, shugabar hukumar shige da fice mai kula da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), Aisha Shehu Nda, ta bayyana cewa ziyarar da suka kai hukumar Alhazai na da nufin karfafa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin saukaka tafiyar da al’amuran Hajji.
A matsayin girmamawa, Aisha Shehu Nda ta karrama Darakta Janar na hukumar Jin Dadin Alhazai da lambar yabo.
