Connect with us

News

Wani Hatsarin Mota Ya Sake Faruwa A Gadar Karu A Abuja, Kwana Daya Bayan Mutuwar Mutum 10

Published

on

1742506488521

Wani sabon hatsarin mota ya sake faruwa a kusa da gadar Karu, kan titin Abuja-Keffi Expressway, sa’o’i 24 bayan hadarin babbar mota dauke da iskar CNG da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 10.

A cewar rahotanni, wannan sabon hatsarin ya afku ne da misalin karfe 3:54 na yammacin Alhamis, inda babbar mota dauke da takin zamani ta yi karo da wata mota kirar Hijet da kuma wata babbar mota dauke da yashi (tipper).

Advertisement

Maniyyata 3,155 Sun Yi Rijistar Hajjin Bana Daga Jihar Kano

Sai dai, a cewar shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar bada agajin gaggawa ta Abuja (FCT Emergency Management Department), Nkechi Isa, babu asarar rai a wannan hatsarin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Isa ta bukaci direbobi da su rika taka-tsantsan yayin tuki, tare da bayyana cewa jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) suna aiki don kawar da ragowar motoci a wurin domin hana cunkoso.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending