Connect with us

News

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Gungun ‘Yan Fashi da Masu Garkuwa Da Mutane Guda 10 A Kano

Published

on

images

 

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Gungun ‘Yan Fashi da Masu Garkuwa Da Mutane Guda 10 A Kano

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasara bayan cafke mutane goma da ake zargi da aikata garkuwa da mutane da fashi da makami. Haka zalika, jami’an tsaro sun kwato makamai da kudi har Naira miliyan hudu da dubu dari takwas da hamsin (N4,850,000).

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, yana kan bakin kokarinsa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a Kano.

Advertisement

Wani Hatsarin Mota Ya Sake Faruwa A Gadar Karu A Abuja, Kwana Daya Bayan Mutuwar Mutum 10

Bisa bayanai, a ranar 18 ga Maris da misalin karfe 11 na dare, wasu ‘yan fashi sun kutsa wani gida a Badawa Layout, inda suka raunata mazauna tare da yunkurin sace motoci da wasu kadarori. Sai dai cikin gaggawa, jami’an tsaro sun kai dauki inda suka kama Awwal Hassan Ibrahim (29) da Suleiman Umar (24), dukkansu daga Jihar Filato, tare da kwato bindigar Beretta mai alburusai biyu daga hannunsu.

Haka kuma, a ranar 18 ga Maris da misalin karfe 11 na safe, an samu rahoto kan wani mutum da ke yawo da bindiga a cikin mota. Bayan bincike, an kama Shuaibu Yakubu, wanda aka fi sani da Dan Bula Bula, a Kadawa, Kano, tare da bindigar AK-47 mai harsasai 12 da mota kirar Pontiac Vibe, ja launi.

Advertisement

A ci gaba da kokarin yakar laifuka, a ranar 19 ga Maris, Rundunar Rapid Response Team (RRT) ta cafke Friday Bitrus (38) da Daniel Samuel (25) a unguwar Zango, Kano, tare da kwato bindiga kirar gida, harsasai biyu da adda mai kaifi.

Baya ga haka, a ranar 8 ga Maris, wani mazaunin garin Zakirai, Gabasawa LGA ya kai rahoto cewa an sace Muhammad Bello (21), inda masu garkuwan suka nemi kudin fansa N15,000,000. Bayan bincike mai zurfi, jami’an Anti-Kidnapping Squad karkashin CSP Bala Shuaibu sun kama mutane biyar da ake zargi tsakanin ranar 11 zuwa 18 ga Maris. Wadanda aka kama sun hada da Tukur Lawal (Maikudi) mai shakarau 20, Ado Usman (Ruwa), mai shakarau 30, Sunusi Surajo, mai shakarau 27, Ummulkhairi Ibrahim,mai shakarau 19, Habiba Shuaibu, mai shakarau 18

Advertisement

An ceto wanda aka sace a ranar 17 ga Maris, tare da kwato kudi N4,850,000 da bindiga kirar gida daga hannun masu laifin.

Dukkan wadanda aka kama suna karkashin bincike a Sashen CID na Rundunar ‘Yan Sanda ta Kano, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.

Advertisement

Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjinawa kokarin jami’an da suka samu nasarar kama wadannan miyagu. Ya kuma jaddada kudirin rundunar na ci gaba da yaki da dukwani nau’i na laifi a Kano.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending