News
Hukumar Shari’ah Da Kungiyar WAMY Sun Shirya Shan Ruwa Na Musamman Ga Wadanda Suka Musulunta A Kano
Hukumar Shari’ah ta Kano tare da haɗin guiwar ƙungiyar World Assembly of Muslim Youth (WAMY) sun shirya taron shan ruwa ga wadanda suka karɓi addinin Musulunci a ranar Lahadi 23 ga Ramadan. Taron ya gudana a harabar hukumar, karkashin jagorancin Mukaddashin Shugaban Hukumar, Sheikh Ali Danabba.
Hukumar ta kuma ayyana ranar 15 ga Ramadan a matsayin ranar da za a dinga shiryawa sabbin Musulmi irin wannan taro a kowace shekara. Sheikh Ali Danabba ya nuna godiya ga Gwamnatin Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kuma ƙungiyar WAMY bisa gudummawar da suka bayar don tabbatar da nasarar shirin.
NDLEA Ta Kama Wata Mata Mai Shekaru 40 Da Robobin Hodar Iblis 424 A Kano
Taron ya samu halartar shugabannin hukumar da na ƙungiyar WAMY, tare da wasu manyan baki. Wakilin Shugaban WAMY, Alhaji Sanusi, ya bayyana jin daɗinsa da yadda shirin ya gudana, inda ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da tallafa wa Musulmi a duniya.
Daya daga cikin sabbin Musulman, A’isha Suraj, ta bayyana farin cikinsu da yadda ake karrama su, tana mai cewa: “Lalle addinin Musulunci addini ne mai dadi.”
Shugaban Hukumar, Dr. Sani Ashir, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa waɗannan sabbin Musulmi don ƙarfafa su a addini. Ya kuma tabbatar da cewa shirin na shekara mai zuwa zai zama na musamman.
A nasa jawabin, kwamishina na daya a hukumar, Gwani Hadi, ya yi kira ga al’umma da su taimaka wajen aurar da sabbin Musulman, yana mai cewa: “Babu irin kalar da ba a da ita a wannan hukuma.”
A karshe, ya yi addu’ar zaman lafiya da ci gaban jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
