Connect with us

News

YANZU-YANZU: Gwamna Edo Ya Ziyarci Kano, Ya Ba da Tabbacin Adalci Kan Kisan Mafarauta 16

Published

on

FB IMG 1743429065225

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyarar jaje ga Gwamnatin Kano da iyalan mafarauta 16 da ’yan bindiga suka kona har lahira a garin Uromi na Jihar Edo.

Da yake jawabi a gidan Gwamnatin Kano, Okpebholo ya bayyana alhini kan lamarin, inda ya tabbatar da cewa mutane 14 daga cikin wadanda ake zargi sun shiga hannu, kuma za a tabbatar da an yi adalci ga iyalan mamatan.

Advertisement

Shugabar Kwamitin Afuwa Ta Kano Ta Bukaci Al’umma Su Taimakawa Daurarru

Shi ma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Gwamnatin Edo da ta tabbatar an hukunta wadanda suka aikata kisan. Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bayyana fuskoki da sunayen wadanda aka kama, tare da neman a biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa ransu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending