Connect with us

News

Bankin Duniya Ya Bai Wa Najeriya Sabon Bashin Dala Biliyan 1.08 Don Bunkasa Ilimi da Walwala

Published

on

the world bank

 

Bankin Duniya ya amince da sabon bashin dala biliyan 1 da miliyan 8 ga Najeriya, kamar yadda ya bayyana a Jaridar THE GUARDIAN ta ruwaito.

Advertisement

A cewar bankin, kudaden za a yi amfani da su ne wajen bunkasa harkokin ilimi da kuma kyautata walwalar jama’a, musamman a fannonin jin dadi da ci gaban al’umma.

Mahaifin Dan Bijilanti Da Aka Kashe A Tawagar Sarkin Kano Ya Bukaci Adalci Da Diyya

Tun farkon wannan shekara, gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na ciyo bashin dala biliyan 2 da miliyan 200 domin gudanar da wasu manyan ayyuka na raya kasa.

Advertisement

A shekarar da ta gabata, Najeriya ta karbi bashin dala biliyan 2.5 daga Bankin Duniya, wanda ya kai kusan Naira tiriliyan 3.5.

A halin yanzu, jimillar bashin da Najeriya ke bin Bankin Duniya ya kai dala biliyan 17 da miliyan 100, wanda ke nuna yadda kasarnan ke dogaro da rancen kasashen duniya don bunkasa tattalin arziki da cigaban al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending