News
Dakarun Soji Sun Kashe Wasu Fitattun Shugabannin ‘Yan Bindiga Guda Uku A Zamfara
Dakarun sojin Najeriya sun kashe wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga guda uku — Auta Jijji, Dankali da Sagidi — a wani samame da suka kai a kauyen Mai Kwanugga da ke Karamar Hukumar Talata Mafara a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru da misalin karfe 1:30 na dare ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, lokacin da dakarun da ke sintiri suka gamu da daruruwan ‘yan bindiga dauke da makamai suna kai hari kan kauyen.
An ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne a kan babura suna harbi da kona gidaje. Sai dai sojojin sun fatattake su tare da kashe da dama daga cikinsu, ciki har da shugabanninsu guda uku da hukumomi suka dade suna nema ruwa a jallo.
Sojoji sun ce sun kwato bindigogi da dama da kuma harsasai daga wajen ‘yan ta’addan.
Bayanai sun ce mutum biyu daga cikin mazauna kauyen sun jikkata sakamakon harbin bazata.
A wani bangare, dakarun soji sun tarwatsa wata zanga-zanga a Kaura Namoda da wasu matasa suka yi sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan fashi da garkuwa da mutane a yankin.
Matasa sun toshe hanya da tayoyi suna neman gwamnati ta dauki mataki. Sai dai jami’an tsaro sun shawo kan lamarin ba tare da amfani da karfi ba.
Rundunar soji ta ce yanzu an samu kwanciyar hankali a yankunan da lamarin ya faru, kuma suna ci gaba da sintiri domin hana faruwar wani abu makamancin haka.
Kisan Auta Jijji, Dankali da Sagidi na daga cikin manyan nasarori da dakarun Najeriya suka samu a yaki da ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
