Connect with us

News

‎Kanawa Sun Shiga Ruɗani: Waye Galadiman Kano na Gaskiya?

Published

on

images (1)

Yau Juma’a birnin Kano ya shiga cikin ruɗani bayan da sarakunan da ke ikirarin zama Sarakunan Kano biyu suka naɗa Galadima biyu dabam-dabam, lamarin da ya bar al’umma cikin tambaya kan wanene Galadiman Kano na gaskiya.

‎Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya naɗa ɗan uwansa, Sunusi Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano, yayin wata walima da aka gudanar a fadar masarautar Kano da ke Nasarawa.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kashe Wasu Fitattun Shugabannin ‘Yan Bindiga Guda Uku A Zamfara

‎A lokaci guda kuwa, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, ya naɗa ɗan uwan mahaifinsa, Munir Sunusi, a matsayin Galadiman Kano a wani biki da ya gudana a fadar Kofar Kudu, wanda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarta.

‎Wannan sabani ya biyo bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, wanda ya bar gurbin da yanzu bangarori biyu ke takara akansa.

Advertisement

‎Masu sharhi na ganin cewa wannan naɗe-naɗen biyu zai iya jefa masarautar Kano cikin wani sabon rikici, musamman ganin yadda al’umma suka rabu kashi biyu – wasu na tare da Aminu Ado Bayero, yayin da wasu ke goyon bayan Muhammadu Sunusi II.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending