News
Atiku: Ba Kai Za Ka Yanke Wa Matasa Shawara Ba — Adnan Ya Fadawa Baba-Ahmed”
Tsohon dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kano, Adnan Mukhtar Tudun Wada, ya kalubalanci tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, yana mai cewa bai da ikon yanke shawara a kan matasan Najeriya.
Adnan ya yi wannan jawabi ne a wata sanarwa da ya fitar a Kano, inda ya bayyana cewa kiran da Baba-Ahmed ya yi na cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya janye daga takarar shugabancin kasa, ba daidai ba ne.
“A gaskiya wannan magana ta Baba-Ahmed ba ta dace ba, kuma ba shi da hurumin yanke wa matasa shawara. Shi da kansa ya karbi mukamin da bai dace da shekarunsa ba a matsayin mai ba Mataimakin Shugaban Kasa shawara, amma yau yana ce wa wasu su janye don a bai wa matasa dama,” inji Adnan.
Ya ce matasa sun isa su fadi albarkacin bakinsu ba tare da wani ya musu jagora ba. “Ni na tsaya takara ina da shekaru 26. Baba-Ahmed ya rike mukamai da dama a matashin sa, amma bai taba ba da damar da yake kira a yanzu ba,” inji shi.
Adnan ya ce ba a kan shekaru ne shugabanci ba, amma a kan cancanta da jajircewa wajen hidimtawa kasa.
“Maganar da ya yi wa Atiku cewa ya janye ba wai shawara ba ce, cin mutunci ne . Idan har matasa za su jagoranci kasa, to su nuna bambanci a inda aka ba su dama kamar gwamna da ‘yan majalisa. Amma abin ba haka yake ba,” inji shi.
Ya ce Atiku yana bai wa matasa dama tun lokacin da yake mataimakin shugaban kasa, kuma har yanzu shi kadai ne jagoran adawa da ke bayyana ra’ayinsa a fili.
Adnan ya kuma zargi Baba-Ahmed da kokarin komawa kusa da Atiku bayan ya ci amanarsa a baya. Ya ce, “Ina kalubalantar Baba-Ahmed ya fadi sunan matashi daya da zai iya daukar nauyin adawa da wannan gwamnati kamar Atiku.”
A karshe, Adnan ya bukaci ‘yan Najeriya su goyi bayan Atiku Abubakar, yana mai cewa shi ne kadai dan adawar da ke da kwarin gwiwar tunkarar gwamnatin Shugaba Tinubu.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
