Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Kama Awaki Kan Zargin Cinye Bishiyoyi A Titunan Jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta kama wasu awaki da ake zargi da lalata bishiyoyin da aka dasa domin ƙawata birnin Kano da yaƙi da sauyin yanayi.

Bishiyoyin dai gwamnatin ta dasa su ne a ƙarƙashin shirin Urban Renewal Project da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ke jagoranta, kuma aikin ya fara ne a kan titin Lodge Road da Race Course.

Advertisement

Matar Aure Ta Kai Mijinta Kotu Saboda  Zargin Soyayya da Mage

Kwamishinan Ma’aikatar, Dr. Dahir M. Hashim, ya ce za a ci gaba da aikin ne har sai an dasa bishiyoyi a manyan titunan Kano baki ɗaya.

Ya ce shirin na da nufin rage zafin rana da gurbacewar iska, da kuma ƙawata birnin domin inganta rayuwar al’umma.

Advertisement

Sai dai ya koka kan yadda wasu ke barin awaki suna cin bishiyoyin da aka dasa. “Mun samu rahoto cewa wasu na barin awaki su yawo suna cin bishiyoyin. Wannan abin ba za mu lamunta ba,” in ji shi.

Dr. Hashim ya ce tuni aka kama wasu daga cikin awakin da ke barna kuma an killace su a Zone I.

Advertisement

Ya kuma roƙi al’umma su ba da haɗin kai domin ganin an cimma nasarar shirin. “Muna kira ga jama’a da su ba mu goyon baya domin dorewar wannan aiki,” in ji Kwamishinan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending