News
’Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Tsanyawa
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sake kai hari a garin ‘Yan Soyawa da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa dake jihar Kano a daren jiya, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da ruɗani.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan hari shi ne karo na uku cikin ‘yan makonnin nan, lamarin da ke ƙara tayar da hankali musamman ganin yadda masu garkuwa da mutane ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin.
Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Ayyana Ranar Litinin A Matsayin Ranar Hutu
A harin farko, ‘yan bindigar sun sace wani magidanci inda suka bukaci fansar naira miliyan bakwai (₦7m). Sai dai bayan an biya kudin, sai suka sake kiran ‘yan uwansa suna neman karin miliyan biyar (₦5m). Abin takaici, a yayin kai kudin fansar na biyu, sai suka sake kama ɗan mutumin da ya kai, inda suka ƙara neman wani miliyan bakwai (₦7m) a kansa.
Wani mazaunin garin da ya buƙaci a sakaya sunansa saboda tsaro ya shaida wa AREWA RADIO cewa:
> “Yanzu haka mutane da dama sun bar gidajensu sun tsere cikin daji. Mun shafe daren jiya ba barci, domin harbin bindiga ya cika gari.”
Ya ƙara da cewa, tun bayan fara hare-haren, babu wata tsayayyar doka ko mataki da hukumomin tsaro suka ɗauka da zai hana sake faruwar haka.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar ba, kuma ba a tantance adadin waɗanda suka jikkata ko abin da ya lalace ba.
Al’umma na ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kawo ƙarshen waɗannan munanan ayyuka da suka addabi yankin.
