Connect with us

News

‎Farfesa Dahiru Sale: Za Mu Tabbatar Kano Ta Ci Gajiyar Shirin TVET ‎

Published

on

IMG 20250601 WA0004

Sakataren Zartarwa na Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Kano (STSB), Dahiru Sale Muhammad wanda ke  Nema zama  Farfesa, ya ce gwamnatin Kano za ta tabbatar da cewa matasan jihar sun amfana da shirin horar da matasa kan sana’o’in fasaha (TVET) da gwamnatin tarayya ta kaddamar a Abuja.

‎Farfesa Dahiru ya bayyana hakan ne bayan halartar bikin bude Taron Kasa na Ilimin Fasaha da Sana’o’i (TVET) da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Advertisement

‎’Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Tsanyawa ‎ ‎ ‎

‎Ya ce shirin zai taimaka matuka wajen rage rashin aikin yi da matasa ke fama da shi a fadin kasar nan.

‎“Mun ga yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke goyon bayan ilimi a Kano, kuma muna da tabbacin cewa za mu dauki matakin da ya dace domin ganin matasanmu sun amfana da wannan dama dari bisa dari,” in ji shi.

Advertisement

‎Ya kuma bukaci shugabannin makarantu da malamai su kara azama wajen taimakawa gwamnati da hukumar STSB domin ganin an koyar da matasa sana’o’in da za su dogara da kansu.

‎Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Ilimi, Karamin Ministan Ilimi, Ministan Kwadago da Matasa da Wasanni, da wasu kwamishinoni da shugabannin makarantu daga jihohi daban-daban na kasar.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending