Connect with us

News

Jigawa: Gwamnati Ta Bankado Ma’aikatan Bogi 7,000 Da Ke Karɓar Albashi

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta gano fiye da ma’aikata 7,000 na bogi da ke karɓar albashi ba bisa ka’ida ba a lokacin da ake gudanar da tantance ma’aikatan gwamnati a fadin jihar.

Kwamishinar Kuɗi ta jihar, Hajiya Hannatu Sabo, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, a wani bangare na bikin cikar Gwamna Umar Namadi shekaru biyu da hawa karagar   mulki.

Advertisement

Majalisar Matasan Arewa Ta Bukaci Matasa Su Guji Tada Hankali A Ya Yin  Bukukuwan Sallah 

A cewar ta, ma’aikatan bogin sun kasa bayyana domin tantancewa, wanda hakan ya nuna cewa ba su da tushe ko sahihancin aiki a karkashin gwamnatin jihar, dalilin da ya sa aka cire su daga jerin masu karɓar albashi.

Kwamishinar ta bayyana cewa wannan nasara ta samo asali ne sakamakon jajircewar gwamnatin jihar wajen yakar duk wata kafa ta zamba da kuma share fagen inganta tsarin gudanar da ayyuka a ma’aikatun gwamnati.

Advertisement

Ta kara da cewa, domin cike gibi da hakan ya haifar, gwamnatin ta dauki sababbin ma’aikata karkashin shirye-shiryenta na J-Teach, J-Health, da J-Agro.

Hajiya Hannatu ta bayyana cewa Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da ke biyan cikakken sabon tsarin albashi ga ma’aikata kafin 25 ga kowane wata, wanda hakan na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka don kare walwalar ma’aikata.

Advertisement

Ta kuma bayyana cewa ana samun karin kudade daga gwamnatin tarayya, lamarin da ke taimakawa wajen aiwatar da manyan ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma a fadin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending