Connect with us

News

DA DUMI-DUMI: Tsohon Babban Alkalin Ƙasa, Mohammed Uwais, Ya Rasu Yana Da Shekaru 89 A Duniya.

Published

on

Tsohon Babban Alkalin Ƙasa (CJN), Mai Shari’a Mohammed Lawal Uwais, ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.

Wata majiya daga cikin iyalansa ta tabbatar da rasuwar tasa a safiyar yau Jumma’a, a birnin Abuja.

Advertisement

An Gano Bindiga A Gidan Wanda Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano 

Mai Shari’a Uwais ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu shari’a da Najeriya ta taɓa yi, inda ya shugabanci Kotun Koli daga shekarar 1995 zuwa 2006, kafin ya yi ritaya daga aiki.

An haifi marigayin ne a ranar 12 ga watan Yuni, shekarar 1936. Bayan ritayarsa daga matsayi na Babban Alkalin Ƙasa, gwamnatin tarayya ta damƙa masa jagorancin Kwamitin Gyaran Zaɓe a shekarar 2008 – wanda ya fitar da muhimmin rahoto da har yanzu ake dogaro da shi wajen nazari kan tsarin gudanar da zaɓe a Najeriya.

Advertisement

Majiyar ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa domin gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Jaridar INDA RANKA na addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya bai wa iyalansa da ‘yan uwa da abokan arziki haƙuri da juriya.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending