News
Gwamnatin Kano Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kasa Akan Bunkasa Fannin Kirkire-Kirkire
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da karɓar bakuncin wani muhimmin Taron Kasa kan Bunkasa Fannin Kirkire-Kirkire a Najeriya, domin karfafa gwiwa da habaka rawar da fannin ke takawa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa.
Wannan mataki ya biyo bayan wani ƙuduri mai ƙayatarwa da ƙungiyar Kannywood Foundation ta gabatar, inda ta jaddada muhimmancin jihar Kano a matsayin cibiyar al’adu da kirkire-kirkire a Arewacin Najeriya.
Ce-Ce-Ku-Ce Ya Barke Akan Shirin Wike Na Ginin Sabuwar Hedikwatar INEC
A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar, ya bayyana cewa taron zai kasance wata babbar kafa ta musayar ra’ayi da dabaru, domin amfani da dimbin damammakin da ke cikin fannin kirkire-kirkire.
Fannin ya ƙunshi sassa da dama kamar fina-finai, dinki da kayan kawa, sana’o’in hannu, waka da adabi, da fasahar zamani.
A cewar sanarwar, an shirya taron ne domin gano hanyoyin da za su inganta ci gaban fannin da kuma amfani da shi wajen ƙara wa tattalin arziki kuzari.
Ana sa ran taron zai jawo manyan masu ruwa da tsaki daga cikin gida da waje, ciki har da hukumomin gwamnatin tarayya, kungiyoyin masu zaman kansu, masu zuba jari, da manyan kamfanonin dijital irin su Netflix da Amazon.
Kwamishina Waiya ya ce, “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa Kwamitin Shirya Taro (LOC) wanda ke kunshe da wakilai daga gwamnati, ‘yan kasuwa, kungiyoyin kirkire-kirkire, sarakunan gargajiya, da masana daga manyan jami’o’i domin tabbatar da shirin ya gudana cikin nasara.”
Ya kara da cewa, “Wannan taro ba wai na al’ada ba ne kawai, amma wata dabarar gwamnati ce domin ɗaga matsayin Jihar Kano a gaban gaba na fannin kirkire-kirkire a Najeriya.”
Ya bayyana cewa masana’antar Kannywood da sauran fannonin fasaha daga Kano na samun karbuwa a duniya, kuma wannan taro zai ƙara haɓaka damar matasa da sauran masu fasaha su taka rawar gani a fagen cigaba da tattalin arziki.
