Connect with us

News

‎Barau Ikon Allah: Siyasar Da Aka Gina A Kan Haƙuri Da Hikima

Published

on

barau

DAGA ABBA ANWAR, KANO

‎A halin yanzu, tambayar da ke yawo a tsakanin masu ruwa da tsaki a siyasar Kano ita ce: Shin Sanata Barau I. Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Ƙasa, shi ne sabon jagoran jam’iyyar APC a Jihar Kano?

‎Ko shakka babu, kasancewarsa dan siyasa mafi girma a matakin zabe daga Jihar Kano a gwamnatin tarayya na nuni da cewa yana da babban tasiri a tsarin rarraba madafun iko da karfin tasiri a cikin jam’iyya da wajen ta.

Yaran Mu Basa Iya Zuwa Makaranta Idan Anyi  Ruwan Sama Sabida Lalacewar Hanya da Magudanan Ruwa  — Al’ummar Hotoron Arewa

‎Tun bayan komawar APC daga mulki a jihar Kano, wasu daga cikin na kusa da tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyya na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje (CON), suka fara yin watsi da Sanata Barau, ko kuma su rika tafiya da tsarin watsar da shi cikin rashin adalci.

‎Abin takaici, irin waɗannan mutane ne suka yi shiru ko janye hannu a lokutan da tsohon gwamnan ke bukatar kariya da tallafi daga hare-hare da kalaman cin mutunci daga magoya bayan adawa. Akwai lokacin da shugaban karamar hukumar Nassarawa a baya, Auwal Shu’aibu Aranposu, ke caccakar tafiyar Ganduje, amma masu amfani da kafafen sada zumunta da ke kusa da tafiyar suka yi kunnen uwar shegu. Sun yi hakan ne saboda tsarin ba ya tsinana musu komai. Bilhasali ma, wasu daga cikinsu sun ma fi amfanar Aranposu, duk da cewar ya na jam’iyyar adawa ta NNPP. Amma daga bangaren APC, masu kula da harkokin yada labaran jam’iyyar daga jikin Ganduje sun dauke su bare marasa amfani.

Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a lokacin zabukan fidda gwani da aka gudanar a Abuja, inda aka yi wa wasu daga cikin magoya bayan Dr. Abdullahi Umar Ganduje, musamman masu aiki a fannin kafafen sada zumunta, Amman daga baya a ka cire sunayen su dan ba a son su dan karu da allowance da a ke bayar wa

Advertisement

mutanen da su ka aiki wajen zaben fidda gwani din akwai yan social media din mu da a ka sa dan yin aikin zaben. Amman daga baya a ka cire sunayen su dan ba a son su dan karu da allowance da a ke bayar wa

 

‎Lokacin da Ganduje ke kammala wa’adinsa na gwamna, ya nuna sha’awar tsayawa takarar Sanata daga Kano ta Arewa, wato mazabar Sanata Barau. Wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce da rudani cikin tafiyar, wanda hakan bai rasa nasaba da masu kwaɗayin rikici da tada jijiyar wuya.

‎Sai dai, tare da irin jajircewar Sanata Barau da kuma goyon bayan manyan jiga-jigan jam’iyyar daga matakin ƙasa, ya sake samun tikitin takararsa, Sai kuma Ganduje ya mara masa baya wajen cin zaben. Kamar yadda ya yi masa a baya

‎Bayan Ganduje ya hau matsayin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, wasu sabbin masu kwaɗayi suka rika yawo da ra’ayoyi marasa tushe, da nufin kawo rarrabuwar kawuna tsakanin shi da Sanata Barau. Sai dai su kansu sun gane daga baya cewa irin wannan danyen aiki ba zai kai su ko’ina ba.

‎Daga bisani, Barau da Ganduje suka haɗa kai wajen fuskantar gwamnatin NNPP mai mulki a Kano. A kowane lamari da ya shafi gwamnati ko siyasa a jihar, ana jingina shi da sunan Ganduje – ko da bai da hannu a ciki. Wannan ya nuna yadda tasirinsa ya wanzu a zukatan masu mulki da talakawa baki ɗaya.

Advertisement

‎Amma da fitowar Barau a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai da kuma Shugaban Majalisar ECOWAS na farko daga Najeriya, hankulan masu adawa suka karkata zuwa gare shi. A yanzu shi ne ke fuskantar suka, shisshigi da adawa daga bangaren jam’iyyar NNPP da ke mulki a Kano.

‎Daga cikin gida ma, wasu da suka dade suna kallon Barau a matsayin wanda ba ya da karfin siyasa, sun fara canza ra’ayinsu. Wasu suna kokarin dawo da zumunci, wasu kuwa na fakewa da suna jam’iyya suna rura wutar rigima. Amma Sanata Barau ya riga ya fahimci dabi’un mutane daban-daban, kuma yana da tsari da fahimtar wanene a yi hulɗa da shi da wanene ba.

‎Tun kafin wannan lokaci, Barau ya shafe shekaru fiye da arba’in a cikin harkokin siyasa. Wannan ya ishe shi matsayin gogaggen ɗan siyasa wanda ya san inda ake nufa da hanyar da za a bi.

‎Yanzu haka, yawancin ‘yan jam’iyyar APC – na gaskiya da na kwaɗayi – sun fara karkata zuwa ga Sanata Barau. Kuma a matsayin sa na mai kwarewa, Barau yana tafiya da tsarin sanin wanene da menene a hannunsa. Yana da ƙwarewa wajen tantance nagarta da riƙon amana.

‎Abin da ya kamata a fahimta shi ne: APC ba jam’iyyar mutum guda ba ce. Jam’iyya ce da ke ci gaba da zama ginshiki a siyasar Najeriya saboda tsari da daraja, ba wai domin mutum guda ba.

‎A karshe, Sanata Barau I. Jibrin – wanda yanzu shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai da kuma Shugaban Majalisar ECOWAS na farko daga Najeriya – yana ci gaba da shigowa zukatan jama’a a matsayin wanda Allah ke tafiyar da tafiyarsa.

Advertisement

‎Barau: Ikon Allah.

‎Abba Anwar ya rubuto daga Kano — 3 Yuli, 2025.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending