Connect with us

News

Yaran Mu Basa Iya Zuwa Makaranta Idan Anyi  Ruwan Sama Sabida Lalacewar Hanya da Magudanan Ruwa  — Al’ummar Hotoron Arewa

Published

on

IMG 20250703 WA0034

Al’ummar unguwar Uwar Kwari da ke Hotoron Arewa a karamar hukumar Nasarawa dake Jihar Kano, sun koka kan yadda lalacewar hanya da toshewar magudanan ruwa ke jefa rayuwar al’umma cikin hadari, tare da hana yaran su zuwa makaranta musamman a lokacin ruwan sama.

Sun ce duk da kokarin da suka yi na gyaran hanyar da kansu tare da hadin gwiwar malamai da kungiyoyi, ruwan sama da ya zubo a kwanakin baya ya lalata komai, inda ya dawo da su baya fiye da yadda lamarin ya kasance a da.

Advertisement

Barau FC Ta Sauka Asaba Domin Fafatawa A Gasar NNL Super 8

“Mun tara kudi muka gyara, amma ruwan sama ya wanke duk aikin. Yanzu idan an yi ruwan sama, yaran mu ba sa iya zuwa makaranta saboda hanya ta lalace matuka,” inji daya daga cikin dattawan yankin.

Malaman makaranta da iyaye sun bayyana damuwa kan yadda wannan matsala ke barazana ga cigaban karatu da lafiyar yaran, inda suka ce hakan na iya jefa yankin cikin matsanancin koma baya a fannin ilimi.

Advertisement

Wani mazaunin yankin  ya bayyana cewar yanzu haka yaran su basa iya zuwa makaranta sakamakon ruwa ya malale ko ina a hanyar saboda rashin magudanar ruwa kuma ya bayyana cewar aikin ya fi karfin su.

Shima wani magidanci ya bayyana cewar yanzu haka yayansa biyar suna fama da zazzabin maleriya sakamakon cizon sauro saboda kwanciyar ruwa a kofar gidan sa.

Advertisement

Al’ummar yankin sun bukaci gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugaban karamar hukumar Nasarawa da su kawo dauki cikin gaggawa domin gyaran hanya da magudanan ruwa kafin matsalar ta rikide zuwa wata babbar annoba.

Sun ce gyaran hanyar da magudanan ruwa ba wai alfarma ba ne, hakkinsu ne da ya dace gwamnati ta kulawa da shi don kare rayuka da makomar ilimin yara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending