Connect with us

Politics

Atiku Abubakar Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Published

on

IMG 20220913 WA0014

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), yana mai danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar a halin yanzu.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya rubuta da kansa, wacce ya aikawa shugaban jam’iyyar na gundumarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Yi Ajalin Manoma 27 A Wani Sabon Hari A Filato

A cikin wasikar, Atiku ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne saboda rashin tabbas da rikice-rikice da suka dabaibaye jam’iyyar, lamarin da ya ce ya hana ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata a matakin ƙasa.

“Bayan nazari mai zurfi da tuntuba da dama, na yanke shawarar barin jam’iyyar PDP saboda halin rashin daidaito da rashin tabbas da ke ci gaba da kawo cikas ga makomar jam’iyyar,” in ji Atiku a cikin wasikar.

Advertisement

Ya kuma godewa shugabannin jam’iyyar na matakai daban-daban bisa hadin kai da goyon bayan da suka ba shi tun lokacin da ya fara mu’amala da jam’iyyar shekaru da dama da suka gabata.

Ficewar Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP ke fama da rikice-rikicen shugabanci da kuma rikodin rashin jituwa a fadin ƙasar, musamman yayin da ake shirin fara gyare-gyaren cikin gida domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending