News
KAROTA Ta Cafke Direban Da Ya Lalata Shuke-shuken Gwamnati A Kano
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta cafke wani direban mota bisa zargin take dokar hanya da kuma lalata shuke-shuken gwamnati da aka dasa domin kyautata kwalliyar birnin Kano.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a titin Murtala Muhammad, inda direban ya bijire wa ka’idojin zirga-zirga, ya juya ba tare da izini ba, lamarin da ya kai ga matakin murkushe furannin da aka shuka a gefen hanyar domin kawata birnin da kuma kare muhalli.
Mai magana da yawun hukumar KAROTA, Malam Abubakar Ibrahim Sharada, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya bayyana cewa za a gurfanar da direban a gaban kotu bisa zargin karya doka da kuma barnatar da dukiyar al’umma.
“Direban ya aikata babban laifi na zirga-zirga. Za a gurfanar da shi domin zama izina ga sauran masu motoci da ke nuna halin ko-in-kula ga dokokin hanya,” in ji Sharada.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Kano na zuba makudan kudade wajen shuka furanni da itatuwa a birnin domin rage illar sauyin yanayi da inganta lafiyar muhalli, don haka dole ne a kare wannan dukiyar jama’a daga masu gangan lalata ta.
Sharada ya kuma bayyana cewa direban ya nuna rashin da’a ga jami’an KAROTA lokacin kama shi, inda ya nemi tayar da jijiyoyin wuya da musu zagi.
Hukumar KAROTA ta bukaci direbobi da sauran masu amfani da tituna da su bi doka da oda, tare da mutunta kokarin gwamnatin jihar na gyara da kyautata yanayin rayuwa a Kano.
