News
Gwamnatin Kano Da Kungiyoyin Farar Hula Sun Hada Kai Don Yaki Da Tabarbarewar Tarbiyya Da Laifuka
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kaddamar da wani sabon shiri tare da hadin gwiwar kungiyoyin farar hula domin dakile matsalolin tsaro da suka hada da satar wayoyi, shaye-shaye da rikicin matasa a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka yayin wani taron tuntuba da aka gudanar a Gidan Mambayya, inda ya ce gwamnati ta kirkiro wani tsari mai suna “Safe Corridor” domin magance tushen matsalolin rashin tsaro.
Kotu Ta Ɗage Sauraron Ƙarar Da ICPC Ta Kai Shugaban KANSIEC Farfesa Malumfashi
A cewar sanarwar da Sani Abba Yola, Daraktan Harkokin Musamman na Ma’aikatar, ya fitar, Waiya ya ce an shirya taron ne domin tattaunawa da kungiyoyin da ke kusa da al’umma don gano hanyoyin da za a bi wajen shawo kan matsalolin tsaro da tarbiyya a jihar.
“Gwamnati na ganin cewa mafita mai dorewa na farawa ne daga tattaunawa da hadin gwiwa da jama’a. Shi ya sa muka gayyaci kungiyoyin da ke kusa da mutane domin mu saurari ra’ayoyinsu,” in ji Waiya.
Wakilan kungiyoyi sama da 75 ne suka halarci taron, inda suka bayyana dalilan da ke haddasa karuwar laifuka da suka hada da, Rushewar tarbiyyar gida, Yawaitar shaye-shaye, Rashin aikin yi, Raguwar tasirin addini da al’ada, Gibin da ke cikin aikin jami’an tsaro
Sun kuma bayar da wasu shawarwari da suka hada da kafa layin waya na sirri don kai rahoton laifuka, amfani da wasan kwaikwayo da kafafen yada labarai wajen wayar da kai, da kuma hada kai da malamai da shugabannin addini don gyaran halayen matasa.
Mai rikon mukamin Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Inuwa Idris Yakasai, ya ce taron ya zo a lokacin da ya dace, ganin yadda ake samun karuwar laifuka a Kano, musamman satar wayoyi da aikata ta’addanci a titi.
“Wadannan laifuka na haddasa fargaba a tsakanin jama’a, na hana yara zuwa makaranta, kana na kawo koma baya ga tattalin arzikin jihar,” in ji Yakasai.
Ya ce gwamnati ba ta zo da wannan shiri domin zargi ba, sai don neman mafita tare da al’umma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
