News
Danwawu ya tsere bayan wanda ya tsaya masa a kotu ya janye
Rahotanni daga jaridar DAILY NIGERIAN sun bayyana cewa Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ake zargi da kasancewa babban dillalin miyagun ƙwayoyi a jihar Kano, ya tsere daga hannun shari’a, kwanaki bayan da kotun tarayya da ke Kano ta ba shi beli.
Danwawu ya samu belin ne bisa tsayuwar Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, wanda ya gabatar da kansa a matsayin mai tsaya masa.
Sai dai bayan fitar rahoton cewa Kwamishinan ya tsaya wa wanda ake zargi da zama dillalin miyagun ƙwayoyi, ce-ce-ku-ce da suka daga jama’a ya barke a kafafen sada zumunta.
Bayan wannan cece-kuce, majiyoyi sun ce Kwamishinan ya nemi Danwawu cikin gaggawa don ganawa da shi, amma Danwawu ya kashe wayoyinsa, ya guje masa, kuma ya ƙi bayyana kansa. Wannan lamari ya sanya Kwamishinan cikin halin ɗimuwa da rashin tabbas.
A daren Juma’a, Kwamishina Namadi ya fitar da wata wasika zuwa kotu inda ya sanar da janye kansa daga matsayin wanda ya tsaya wa Danwawu.
Ya ce ya dauki wannan matakin ne don kare martabarsa a idon jama’a a matsayin jami’in gwamnati.
Yanzu haka ba a san inda Danwawu ya shiga ba, yayin da ake sa ran kotu da hukumomin tsaro za su ɗauki mataki domin tabbatar da an dawo da shi gaban shari’a.
