News
Matashi Yayi Ajalin Surukarsa Saboda Matsin Lamba Kan Sha’anin Aurensa
Rundunar sa-kai a ƙaramar hukumar Omala da ke jihar Kogi ta cafke wani matashi mai suna Yayu Musa, ɗan shekara 27, bisa zargin kashe surukarsa Atayi Abdul, sakamakon sabani da ya shafi sha’anin aurensa da ‘yarta.
Bayanan da LEADERSHIP ta tattara daga mazauna yankin sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare, ranar Juma’a, a garin Olla.
Wanda ake zargi, Yayu Musa, ya yaudari surukarsa da zargin cewa wasu na satar amfanin gonarta. Da ta bi shi zuwa gonar domin ganin abin da ke faruwa, sai ya dirka mata duka har lahira.
Bidiyon da rundunar sa-kai ta fitar ya nuna gawar mamaciyar na ɗauke da muggan raunuka a jikinta, wanda ke nuna cewa an sare ta da makami mai kaifi kafin a kashe ta.
Bayan aikata kisan, Yayu ya tsere daga yankin, amma rundunar sa-kai ta baza komarta har ta cafke shi a wani gari da ke makwabtaka da Olla.
A cikin bidiyon da aka ɗauka bayan kama shi, Yayu Musa ya amsa cewa ya kashe surukarsa ne saboda yadda ta ke tsoma baki cikin aurensa, tana caccakar sa bisa rashin samun haihuwa da matarsa, Umi Idris.
Ya ce: “Na sadaukar da komai na, har da sayar da babur don neman magani. Amma surukata na cewa ban cancanci auren ‘yarta ba, har ta fara shirin ba wani namiji ita.”
A halin da ake ciki, rundunar ƴan sandan jihar Kogi ba ta fitar da sanarwa kai tsaye kan lamarin ba. Sai dai wani babban jami’in ‘yan sanda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi, kuma an tura shi birnin Lokoja domin ci gaba da bincike.
