Connect with us

News

Gwamnoni 2 Daga Kudancin Najeriya Za Su Shiga Jam’iyyar ADC

Published

on

ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Kudu maso Gabas ta bayyana shirin karɓar gwamnoni biyu masu ci daga yankin.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa reshen Kudu maso Gabas, Chilos Godsent, ya fitar da sanarwar a madadin kwamitin ZWC.

Advertisement

‎Yadda Sauyin Yanayi Ke Jefa Mata Masu Juna Biyu Cikin Hadari”

Ya ce tattaunawa na ci gaba sosai, kuma gwamnonin za su bayyana shirin komawarsu ADC nan ba da jimawa ba.

Chilos ya bayyana cewa shirin na cikin ƙudurin ADC na lashe zaɓen 2027 a Kudu maso Gabas tare da ƙarfafa gabanin babban zaɓe.

Advertisement

Ya kuma ce wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi na shirin ayyana komawarsu jam’iyyar ADC a watanni masu zuwa.

Wani ɗan majalisa ya ce sun yanke shawarar haɗa kai da masu sauyi domin fatattakar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending